?>

Hezbollah: Matakin Da Birtaniyya Ta dauka Kan Hamas Zalunci Ne

Hezbollah: Matakin Da Birtaniyya Ta dauka Kan Hamas Zalunci Ne

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta bayyana matakin da gwamnatin Birtaniyya ta dauka kan kungiyar Hamas a matsayin "kuskure da rashin tausayi" tare da bayyana hakan a matsayin abin takaici da ci gaba da manufofin Birtaniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - ya habarta cewa, kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta bayyana matakin da gwamnatin Birtaniyya ta dauka kan kungiyar Hamas a matsayin kuskure da kuma rashin tausayi, tare da daukar matakin abin bakin ciki na ci gaba da manufofin Birtaniyya da ke goyon bayan makiya yahudawan sahyoniya da manufofinta; Manufofin da suka danganci kisan kai, ta'addanci, kisa da lalata.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kara da cewa: Wannan matakin ba zai shafi al'ummar Palastinu masu tsayin daka ba, da kungiyar Hamas, da Mujahidanta masu daraja da sauran kungiyoyin gwagwarmaya ba, amma za su kara azama wajen tsayin daka da jihadi har zuwa nasara da 'yanci.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta ce tana son gwamnatin Birtaniya ta sake duba akan manufofinta.

Sakatariyar harkokin cikin gida ta Biritaniya, Pretty Patel, ta sanar a ranar Juma'a 19 ga watan Nuwamba a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, an haramtawa kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falasdinu Hamas gaba daya gudanar da ayyukanta a Biritaniya.

Wannan shawarar ta Landan ta faranta wa gwamnatin sahyoniyawan masu kisan gilla harda kananan yara; A martani daban-daban, firaministan kasar Naftali Bennett da ministan harkokin wajen Isra'ila Yair Lapid sun yi maraba da matakin na Birtaniya.

A daya hannun kuma, da dama na ganin matakin a matsayin wani tabbaci na goyon bayan Birtaniyya ga gwamnatin masu aikata laifuka da kuma nuna kyama da munafunci a London.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*