?>

Harin Nakiya Ya Yi Ajalin Jami’an Hukumar Zabe 7 A Nijar

Harin Nakiya Ya Yi Ajalin Jami’an Hukumar Zabe 7 A Nijar

A Jamhuriyar Nijar, jami’an hukumar zabe bakwai ne aka rawaito cewa sun rasa rayukansu, akan wasu uku suka jikkata yayin da motar da suke ciki ta taka wani abun fashewa yau Lahadi.

ABNA24 : Lamarin ya faru ne a yammacin Jihar Tillaberi da ke da iyaka da Mali, kamar yadda gwamnan jihar ya shaida wa kamfanin labarai na AFP.

Babu dai wata kungiya data dauki alhakin kai harin, saidai sanin kowa ne yankin ya yi kaurin suna wajen fuskantar hare hare na mayakan dake ikirari da sunan jihadi.

Yau ne dai al’ummar Nijar da suka tantanci zabe ke kada kuri’a a zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar, tsakanin dan takaran jam’iyya mai mulki Bazoum Mohamed da kuma tsohon shugaba Mahamane Usman, bayan kasa samun wanda ya lashe zaben a zagayen farko.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni