?>

Habasha: Firai Ministan Ya Mika Mulki Ga Ministan Harkokin Waje Ya Tafi Fagen Fama

Habasha: Firai Ministan Ya Mika Mulki Ga Ministan Harkokin Waje Ya Tafi Fagen Fama

Firai ministan kasar Habsha Abiy Ahmed ya mikawa ministan harkokin wajensa harkokin tafiyar da mulkin kasar ya kuma tafi fagen fama inda ya sha alwashin jagorantar sojojin kasar wajen yaki da yantawayen Tigray wadanda suke dab da birnin Adis Ababa babban birnin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tun shekarar da ta gabata ne sojojin gwamnatin Habasha suka farwa yan tawayen Tigray a yankinsu daga arewacin kasar, inda kwace birnin Makella babban birnin yankin na watanni amma daga baya mayakan yankin sun sake dawo da ikonsu kan Makelle sannan suka nosa zuwa babban birnin kasar bayan sun ratsa ta yankin Oromo.

A cikin watan Octoban da ya gabata yan tawayen sun kama sojojin habasha 11,000 a birnin Makelle bayan da sojojin suka mika mai.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*