?>

Gwamnatin Masar Ta Sasanta Da Tsoffin Jami’an Gwamnatin Mubarak Bayan Sun Biya LE Biliyon1.3

Gwamnatin Masar Ta Sasanta Da Tsoffin Jami’an Gwamnatin Mubarak Bayan Sun Biya LE Biliyon1.3

A jiya Asabar ce gwamnatin kasar Masar ta bada sanarwan cewa ta sasanta da tsoffin jami’an gwamnatin Mubarak bayan sun biya lira biliyon 1.3. Jaridar Egypt Today ta nakalto mai gabatar da kara na kasar yana cewa tsohon ministan gidaje na gwamnatin Mubarak Muhammad Ibrahim Soliman a yanzu dan kasuwa da kuma Magdy Rasekh sun biya gwamnatin kasar Lira biliyon 1.3

ABNA24 : Labarin ya kara da cewa mutanen biyu sun sasanta da gwamnatin kasar bayan da kwamitin kwato kudaden jama’a na kasar ya bukaci Solima tsohon ministan gidajen kasar da Rakhe wanda ya reni Alaa Mubarak da su biya wadannan kudade ko je je kaso na shekaru 3 da kuma 5 saboda kudaden jama’a da suka ci.

Ana zargin Soliman da saida filaye a yanki na ‘6 ga watan Octoba’ kan kudaden da basu kai kimarsu na gaskiya ba.

Har’ila yau gwamnatin ta sasanta da wasu da dama daga cikin jami’an gwamnatin da ta shude bayan sun biya kudaden da ake zarginsu da yin sama da fadi da su.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni