?>

Gwagwarmayar Falasdinawa Ta Taka Rawa Wajen Rushewar Gwamnatin Kawancen H.K.Isra’ila

Gwagwarmayar Falasdinawa Ta Taka Rawa Wajen Rushewar Gwamnatin Kawancen H.K.Isra’ila

Jagora a kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Jihadul-Islami ya bayyana cewa: Gwagwarmayar Falasdinawa ta taka rawa wajen rushewar gwamnatin kawance ta Haramtacciyar kasar Isra’ila.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Gwamnatin kawancen Haramtacciyar kasar Isra’ila karkashin jagorancin Naftali Bennett wacce ta kunshi jam’iyyu takwas da na daf da rushewa, don haka ake tunanin maye gurbin Naftali Bennette da Ya’ir Lapid ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar ta Isra’ila a halin yanzu.

Dr Ahmad Al-Mudallal ya bayyana cewa: Dabi’ar gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da rikici da al’ummar Falasdinu ta hanyar zaluntarta ba za ta kai ta ga samun nasara ba, kuma duk gwamnatin da za a kafa a Haramtacciyar kasar ta Isra’ila ba za ta kai labari ba matukar ta zabi bakar siyasar zalunci.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*