?>

Guterres Ya Bukaci A Gaggauta Tsagaita Wuta A Habasha

Guterres Ya Bukaci A Gaggauta Tsagaita Wuta A Habasha

Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci bangarorin dake rikici a Habasha dasu kai zuciya nesa su kuma gaggauta tsagaita Wuta.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Da yake sanar da hakan a wani taron manema labarai a wata ziyarar a Columbia, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bukaci tsagaita wuta a Habashar ba tare da wata wata ba domin ceto kasar.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara shiga zaman dar-dar a kasar ta Habasha, bayan da firaiministan kasar, Abiy Ahmed, ya sha alwashin jagorantar yaki da 'yan tawayen Tigray, wadanda rahotanni ke cewa suna kara dannawa kusa da babban birnin kasar Addis Ababa.

Sanarwar da Abiy ya yi na zuwa ne a daidai lokacin da su ma dakarun 'yan tawayen 'yantar da yankin Tigray suka sanar da cewa suna gab da shiga birnin Ababa.

Kungiyar Tarayyar Afirka na kokarin ganin ta shiga tsakani domin sasanta bangarorin biyu, domin hawa teburin sulhu.

Kasashen duniya da dama musamman na turai da Amurka, na baiwa ‘yan kasashensu shawara su bar Habasha duba da halin da ake ciki.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*