?>

Gungun ‘Yan Kungiyar Da’ish Sun Tsere Daga Gidan Kurkuku A Kasar Siriya

Gungun ‘Yan Kungiyar Da’ish Sun Tsere Daga Gidan Kurkuku A Kasar Siriya

Wasu gungun ‘yan kungiyar ta’addanci ta Da’ish da ake tsare da su a gidan kurkuku garin Riqqa na kasar Siriya sun tsere.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rahotonnin sun bayyana cewa: A safiyar yau Lahadi wasu gungun ‘yan ta’addan kungiyar Da’ish ko ISIS kimanin 30 sun tsere daga gidan kurkukun garin Ar-Riqqa na kasar Siriya, kuma gidan kurkukun yana karkashin kulawar dakarun ‘yan tawayen Siriya ne ta Syrian Democratic Forces da mafiya yawansu ‘yan kabilar Kurdawa ne gami da wasu ‘yan kananan kabilun kasar da suke neman kafa tsarin Tarayya a kasar Siriya.

Rahotonni sun bayyana cewa: Da misalin karfe uku na daren jiya an ji karar harbe-harbe a yankin da gidan kurkukun yake, sannan bayan wayewar garin dakarun kungiyar ‘yan tawayen sun killace yankin da nufin zakulo ‘yan ta’addan ta hanyar gudanar da samame gida-gida.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*