?>

Grossi Ya Gana Da Manyan Jami'an Iran Kan Batutuwa Da Suka Shafi Shirinta Na Nukiliya

Grossi Ya Gana Da Manyan Jami'an Iran Kan Batutuwa Da Suka Shafi Shirinta Na Nukiliya

A ranar jiya Talata ne 23 ga watan Nuwamban 2021, Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya ya gudanar da ziyarar aiki a birnin Tehran na kasar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran Muhammad Islami, da kuma shugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi, sun bayyana cewa sun tattauna kan abubuwa daban-daban da suka shafi batun shirin Iran na nukiliya da kuma yadda za su ci gaba da yin aiki tare.

Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran Muhammad Islami ya bayyana cewa, babu wani abu da ya saba wa ka’ida ko doka a cikin shirinsu na nukiliya, kamar yadda ita kanta hukumar makamashin nukiliya ta sha bayyana hakan a cikin rahotannin da ta fitar a lokuta daban-daban.

Shi ma a nasa abangaren shugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi ya bayyana cewa, ziyarar tasa a Iran tana da matukar muhimmanci, kuma a samu samu tattauna abubuwa da dama da ake da sabani fahimta a kansu tsakanin hukumar ta IAEA da kuma hukumar makamashin nukiliya ta Iran.

Sai dai a daiadi lokacin da ake batun komawa kan teburin ci gaba da tattaunawa domin farfado da yarejejniyar nukiliya ne, a nata bangaren Isra’ila tana barazanar kai hare-hare kan tashoshin nukiliya na Iran, da nufin tsokano wata fitina wadda za ta rusa tattaunawar.

Duk kuwa da cewa Amurka ba ta goyon bayan Isra’ila kan haka, saboda masaniyar da take ita kana bin da zai kai ya komo matukar Isra’ila ta kai wa Iran hari.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*