?>

Ga Alamu An Kama Hanyar Kawo Karshen Rikicin Siyasar Haiti

Ga Alamu An Kama Hanyar Kawo Karshen Rikicin Siyasar Haiti

Firaministan wucin gadi a Haiti, Claude Joseph ya amince mika mulki ga abokin hamayarsa Ariel Henry.

ABNA24 : Ma'aikatar cikin gidan kasar Haiti ta fidda sanarwar cewa, Claude Joseph da ke rike da mukamin Firaministan kasar na wucin gadi tun bayan kisar gilla da aka yi wa shugaban kasar Jovenel Moise zai mika mulkin ga abokin hamayarsa Ariel Henry da ke samun goyon bayan kasashen ketare nan ba da jimawa ba.

Ana sa ran wannan sanarwa ta kawo karshen rikicin neman shugabanci da kasar ta Haiti ke ciki, musamman ma tsakanin wadannan mutanen biyu.

Ariel Henry shi ne wanda marigayi shugaba Moise ya nada firaminista, kwanaki biyu kafin kisansa da ba a kai ga rantsar da shi ba.

Tuni dai wasu kasashen duniya irinsu Amurka, suka yaba da matakin, wanda suka ce zai iya kawo karshen rikicin siyasar kasar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*