?>

Firayi Ministan Habasha Ya Sha Alwashin Mai Da Kakkausan Martani Ga ‘Yan Tawayen Tigray

Firayi Ministan Habasha Ya Sha Alwashin Mai Da Kakkausan Martani Ga ‘Yan Tawayen Tigray

Firayi ministan ƙasar Habasha Abiy Ahmed ya sha alwashin mai da martani ga hare-haren ‘yan tawayen yankin Tigray da ya kira su maƙiya a daidai lokacin da ‘yan tawayen suke ci gaba da ƙaddamar da sabbin hare-hare kan sojojin gwamnati.

ABNA24 : Firayi ministan na Habasha ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce har ya zuwa yanzu yana girmama batun sulhu da zaman lafiya, to sai dai babu yadda za a zuba ido kan waɗannan hare-hare da ake kai wa ba tare da mayar da martani ba. Mr. Abiy ya ce gwamnatinsa ta ɗau matsayar tsagaita wuta daga ɓangare guda ne don ba da dama ga harkokin agaji da ɗauki sai dai ya ce lalle za su mayar da martani da hare-haren ‘yan tawayen wanda ya zarga da amfani da ƙananan yara a matsayin sojoji. Cikin ‘yan kwanakin nan dai dakarun yankin Tigray ɗin suna ci gaba da ƙwace wasu yankuna daga hannun dakarun gwamnatin tun bayan ƙwace garin Mekelle babban birnin yankin da suka yi kwanakin baya.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*