?>

Faransa Zata Sayarwa Kasar Masar Jiragen Yaki Samfurin Rafale Har 30

Faransa Zata Sayarwa Kasar Masar Jiragen Yaki Samfurin Rafale Har 30

Ma’aikatar tsaron kasar Masar ta bada sanarwan cewa kasar Faransa zata sayarwa kasar jiragen yaki samfurin Rafale guda 30 a kan farashin dalar Amurka biliyon 4.5.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa a cikin watan Afrilun da ya gabata ne aka kammala cinikin, sannan jami’an gwamnatin kasar ta Masar zasu kammala sanya hannu a kan wannan cininin a birnin Paris a yau Talata.

Kafin haka dai shugaba Emmanuel Maocron yak i amincewa da sayarwa kasar Masar jiragen yakin don abinda ya kira ayyukan take hakkin bil’adama a kasar.

Banda haka ana saran faransa zata sayarwa kasar ta Masar makamai masu linzami samfurin Safran da dama wadanda kimarsu ya kai uro miliyon 200.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*