?>

Faransa Na Tattaunawa Da Nijar Kan Sabbin Dabarun Tsaro A Yankin Sahel

Faransa Na Tattaunawa Da Nijar Kan Sabbin Dabarun Tsaro A Yankin Sahel

Ministar tsaron Faransa, Florence Parly, na wata ziyara a Jaahuriyar Nijar, mai manufar tattauna sabbin dabarun Faransa na tabbatar da tsaro a yankin Sahel.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Faransa dai na son kara kara karfinta a yankin Sahel tare da hadin guiwar kasashen yankin musamman kasar ta Nijar.

A watan Yunin da ya gabata shugaban faransa Emanuel Macron, ya sanar da shirin rage dakarun faransar a yankin, daga 5,000 zuwa 3,000 ko 2,500 nan gaba.

Aikin dakarun zai maida hankali wajen yaki da ta’addanci da bada horo ga sojojin kasashen yankin tare da hadin guiwar kasashen turai.

Wani batun da ake sa ran Faransar za ta tattauna kan shi sun hada da batun cewa Mali na shirin kulla alaka da wani kamfani mai zaman kansa na Rasha (Wagner) domin horar da sojojin Mali da kuma tabbatar da tsaron lafiyar manyan jami’an kasar.

Kasashen Faransa da Jamus dai sun bayyana cewa zasu sake duba alakarsu ta soji da Mali, muddin dai ya tabbata cewa ta kula wannan yarjejeniya da kamfanin tsaron na Rasha.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*