?>

Falasdinu : An Yi Jana’izar ‘Yar Jaridar Da Sojin Isra’ila Suka Bindige

Falasdinu : An Yi Jana’izar ‘Yar Jaridar Da Sojin Isra’ila Suka Bindige

A Falasdinu, yau Alhamis ne akayi jana’izar ‘yar jaridar nan ta tashar Al’ Jazeera, Shireen Abu Akleh, da aka bindige tana tsaka da aiki yayin wani samamen sojojin Isra’ila a yankin Jenin dake yamma da gabar yamma da kogin Jodan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - An yi jana’izar ce tare da halartar shugaban falasdinawa Mahmoud Abass.

Kisan ‘yar jaridar dai ya janyo tofin Allah-tsine daga bangarori daban daban na duniya a Falasdinu kasancewarta sananiya musamman wajen bada lamarin irin ta’asar da sojojin mamaya na Isra’ila ke aikatawa a yankin.

Falasdinu da Qatar duk sun bukaci binciken kasa da kasa kan kisan ‘yar jaridar, yayin da Isra’ila ta bukaci na hadin gwiwa.

Ministan tsaron Isra’ilar Benny Gantz, ya ce sojojin kasar basu da masaniya game da ainahin yadda aka kashe ‘yar jaridar Shireen Abu Akleh, amma suna bukatar a basu harsashen na bindiga domin gudanar da bincike tare da halartar kwararu daga falasdinu da kuma Amurka.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*