?>

Falasdinawa Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Harin Sojojin Israi’la

Falasdinawa Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Harin Sojojin Israi’la

Taho mu gama ya faru ne a jiya talata bayan da sojojin Isra’ila suka yi amfani da harsashin roba da kuma hayaki mai sa hawaye wajen tarwasta masu zanga-zanga da suka yi cincirindo a kofar arewa ta shiga garin Ramallah.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sun harbe masu zanga-zanga guda 5 da harsashin roba daya kuma an harbe shi akai, yayin da wasu da dama kuma sun samu matsala bayan da suka shaki hayaki mai sa hawaye sa’ilin da rikici ya barke tsakanin falasdinawa da sojoji na Isra’ila bayan da suka kai samame a jami’ar Birzeit tare da cafke wasu dalibai da dama.

Kungiyar bada agaji ta red Cross ta falasdinawa ta bada rahoton cewa wasu ma’aikatanta sun samu raunuka 12 alokacin taho mu magama din da aka yi a kofar shiga ramalla.

Su dai daliban jami’ar sun yi zanga zanga a harabar jami’ar ne domin nuna adawa da kama abokan karantunsu da sojojin Isra’ila suka yi , da kuma yin tir da gwamnatin isra’ila game da cin zarafin kayyakin karatu da sojojinta suka yi .

Maaikatar harkokin wajen Falasdinu da ta ilimi yayi tir a wannan samamen da sojojin Isra’ila suka kai jami’ar Biezeit kuma hakan ya bayyana gaskiyar fuskar gwamnatin Tel’aviv game da zaluntar alummar falasdinu da take yi, kana sun bukaci mdd da sauran masu fada aji na duniya da su dauki mataki na abin da suka kira kassarta ilimi da Isra’ila ke nufin yi a falasdinu.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*