?>

Erdugan Ya Sha Alwashin Fallasa Masu Taimakon ‘Yan Tawayen Kasarsa

Erdugan Ya Sha Alwashin Fallasa Masu Taimakon ‘Yan Tawayen Kasarsa

Shugaban kasar Turkiyya ya sha alwashin gabatar da hujjoji kan yadda kasashe Finland da Sweden suke taimakawa ‘yan tawayen kasarsa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Sabah ta kasar Turkiyya ta watsa labarin cewa: Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdugan ya sha alwashin gabatar da kwararan dalilai da hujjoji kan yadda kasashen Finland da Sweden suke taimaka wa ‘yan ta wayen kasarsa ta kungiyar Kurdawa ‘yan tawaye ta PKK, a yayin zaman taron kungiyar tsaro ta NATO na nan gaba da za a gudanar a birnin Madrid na kasar Spain.

Shugaba Erdugan ya bayyana cewa: Akwai hujjoji da suke tabbatar da cewa; Kasashen na Finland da Sweden suna taimakawa kungiyar Kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta fuskar kudade da kuma siyasa, kungiyar da Turkiyya take daukarta a matsayar ‘yar ta’adda.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*