?>

Duban Mutane Sun Fito Gangamin Bukatar Gyara A Dokokin Mallakar Bindigogi A Kasar Amurka

Duban Mutane Sun Fito Gangamin Bukatar Gyara A Dokokin Mallakar Bindigogi A Kasar Amurka

Dubban mutane ne suka fito kan tituna a birane fiye da 450 a duk fadin Amurka don nuna rashin amincewarsu kan yadda kissan gamagari, ya yawaita a kasar, sannan suka bukaci majalisun dokokin kasar su yiwa wadannan dokoki garan bawul don samun zaman lafiya a kasat.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar Iran ya bayyana cewa a cikin wannan shekara ta 2022 kadai an sami kissan gamagari har sau akalla 254 a duk fadin kasar wanda ya kai ga rasa rayuaksn mutanen da dama.

A birnin Washington D C babban birnin kasar Inda aka gudanar da taron mafi girma magajin garin birnin Muriel Bowser ta y i jawabi a taron in take cewa muna bukatar dokokinmallakar makamai wadanda hankali yake iya amincew ada su. Muriel ta ce kasashen duniya da dama ba sa mummunan rayuwar da muke yi a Amurka.

Matsalar mallakar bindiga dai ta zama babba a Amurka don kamfanonin kera makaman sun damu da riban da suke samu kawai, a yayinsa kasar take kara fadawa cikin kissan gama gari wanda ya hana mutane da dama zaman lafiya a kasar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*