?>

COVID-19: Mutane Biyu Sun Mutu A Nijeriya, Wasu 213 Kuma Sun Kamu Da Korona

COVID-19: Mutane Biyu Sun Mutu A Nijeriya, Wasu 213 Kuma Sun Kamu Da Korona

Hukumar hana yaɗuwar cututtuka a Nijeriya NCDC ta sanar da cewa wasu mutane biyu sun mutu sakamakon kamuwa da cutar nan ta Coronavirus sannan kuma wasu mutane 213 sun kamu da cutar a duk faɗin ƙasar a jiya Litinin.

ABNA24 : Hukumar ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a yayin da take ƙarin haske kan halin da ake ciki a ƙasar dangane da cutar inda ta ce mutane biyu sun mutu sannan wsu 213 kuma sun kamu da cutar.

Hukumar ta ce a halin yanzu yawan adadin wadanda suka kamu da cutar ta COVID-19 a duk faɗin ƙasar sun kai mutane 171,324 sannan adadin waɗanda suka mutu kuma sun kai mutane 2,134, tun farkon ɓullar cutar a ƙasar.

Hukumar ta NCDC ta ce har ya zuwa yanzu dai jihar Lagos ita ce kan gaba a cikin jihohin ƙasar inda cutar ta fi kama mutane inda adadin mutanen da suka kamu da cutar a jiyan Litinin ya kai mutane 157, sai kuma jihar Rivers mai biye mata da mutane 20.

Jihar Filato dai ita ce ta uku da mutane 12, sai kuma jihohin Oyo da Enugu a mataki na huɗu da mutane shida-shida.

Har ila yau kuma sai jihar Gombe mai mutane uku, sai kuma jihohi Bauchi, Imo da Kaduna masu mutane bibbiyu. Edo da Ekiti da Ogun kuma masu mutum guda-guda.

Daga ƙarshe dai hukumar ta bayyana cewar ya zuwa yanzu mutane 164,798 ne suka samu sauki kana kuma aka sallame su daga asibiti sakamakon saukin da suka samu daga cutar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*