?>

COVID-19: Gwamnatin Nijeriya Ta Sanya Jihohi 6, FCT Cikin Wajeje Masu Hatsarin Kamuwa Da Cutar

COVID-19: Gwamnatin Nijeriya Ta Sanya Jihohi 6, FCT Cikin Wajeje Masu Hatsarin Kamuwa Da Cutar

Sakamakon ɓullar sabon nau’in cutar Korona na Delta a Nijeriya da kuma ƙaruwar adadin mutanen da suke kamuwa da cutar a ƙasar, gwamnatin Nijeriyar ta bayyana wasu jihohi six da kuma babban birnin tarayyar ƙasar (FCT), Abuja a matsayin wajajen da suke cikin hatsarin gaske na yiyuwar yaɗuwar cutar a wajen.

ABNA24 : Jihohin da abin ya shafa su ne: Lagos, Oyo, Rivers, Kaduna, Kano, Plateau sai kuma babban birnin tarayyar ƙasar wato Abuja.

A wata sanarwa da aka fitar a safiyar yau Lahadi ɗauke da sanya hannun Shugaban kwamitin yaƙi da annobar ta coronavirus ɗin kuma sakataren gwamnatin tarayyar Nijeriyan, Boss Mustapha, ta ce cikin ‘yan kwanakin nan Nijeriyar tana fuskantar wani yanayi mai tada hankali na ɓullar cutar karo na uku da ya zama wajibi a ɗau mataki.

Boss Mustapha har ila yau ya shawarci jihohin da abin ya shafa da ma ƙasar baki ɗaya da su yi taka tsantsan saboda guje wa yaɗuwar cutar. Haka nan kuma ya kirayi jihohin da su sanya dokar aiki da tsare-tsaren da aka tsara don gujewa yaɗuwar cutar.

Har ila yau kuma kwamitin ya ba da wasu shawarwari don guje wa yaduwar cutar musamman a yayin bukukuwan Idin babbar salla da za a gudanar a ƙasar a ranar Talata mai zuwa. Shawarwarin dai sun haɗa har da yin tsarin da ya dace na gudun cinkoso yayin sallar idi da kuma soke bukukuwan hawan salla da sarakuna suke yi da dai sauran tarurruka.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*