?>

Chadi: 'Yan Tawaye Sun Yi Barazanar Janyewa Daga Tattaunawar Doha

Chadi: 'Yan Tawaye Sun Yi Barazanar Janyewa Daga Tattaunawar Doha

'Yan tawayen da ke tattaunawa a Qatar da hukumomin Chadi don cimma yarjejeniyar zaman lafiya sun yi barazanar ficewa daga tattaunawar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sama da watanni uku da aka bude tattaunawa mai manufar cimma sabon kundin tsarin mulki domin shirya zabe bisa tafarkin demokuradiyya.

A cikin sanarwar bai daya, gungun ‘yan tawayen sun zargi tawagar gwamnati tare da hadin bakin wasu jami’anta da tsaokana, da kuma neman wargaza tattaunawar ta hanyar barazana da tsokana da wulakanci da neman haddasa fada.

‘yan tawayen sun jadadda anniyarsu ta neman cimma yarjejeniyar zaman lafiya, amma sun ce zasu iya ficewa daga tattaunawar idan komi bai canza ba, tare da dora alhakin hakan cuturar tattaunawar ga gwamnatin ta N’Djamena.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*