?>

Burkina Na Bukatar Kawayenta Domin Tsira Daga Halin Da Ake Ciki

Burkina Na Bukatar Kawayenta Domin Tsira Daga Halin Da Ake Ciki

Mai shiga na kungiyar Ecowas kan rikicn Burkina faso, kana tsohon shugaban kasar Nijar, Mahamadu Isufu, ya ce halin da ake ciki a Burkina faso yana da wahaka sosai, kuma kasar na bukatar kawayenta domin fita daga halin da take ciki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mahamadu Isufu, wanda ya kammala ziyara a kasar ta Burkina faso, ya gana da mahukuntan sojin kasar ciki har da shugaban riko laftana kanal Paul Henri Sandaogo Damiba.

Wannan dai ita ce ziyara ta farko ta mai shiga tsakanin na kungiyar ta ecowas kan Burkina faso tun bayan nada shi a ranar 4 ga watan Yuni.

Aikinsa shi ne tattaunawa da sojojin dake mulki a Burkina fason kan wa’adin rikon kwaryar da zasuyi daidai-ruwa-daidai tsaki, domin mika mulki domin mayar da kasar bisa tafarkin demokuradiyya.

Yayin ziyarar mai shiga tsakanin na kungiyar ta Ecowas, ya kasance tare da shugaban kwamitin kungiyar Jean Claude Kassi.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*