?>

Biden Zai Gana Da Yariman Saudiyya Duk Da Zargin Kisan Khashoggi

Biden Zai Gana Da Yariman Saudiyya Duk Da Zargin Kisan Khashoggi

Shugaban Amurka Joe Biden, zai kai wata ziyara irinta ta farko a gabas ta tsakiya a cikin watan Yuli, wacce za ta kai shi a Isra’ila, yankunan falasdinawa da kuma Saudiyya, kamar yadda wani babban jami’in Amurka ya tabbarwa kamfanin dilancin labaren AFP.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Fadar shugaban Amurka ta White House, ta ce yayin ziyarar shugaba Biden zai tattauna batutuwan da suka hada da ci gaba, tsaro, tattalin arziki da dai saurensu.

A Saudiyya wata sanarwa da masarautar kasar ta fitar ta ce bisa goron gayyartar sarki Salmane, shugaba Biden zai ziyarci kasar a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Yuli mai zuwa.

Biden zai kuma gana da yarima mai jiran gado na Saudiyyar MBS, duk da zargin da ake masa kan kisan dan jaridan nan Jamel Khashoggi.

Yayin ziyarar shugaba Biden zai halarci wani taro ta kafar bidiyo da shugabannin kasashen gungun I2-U2, da suka hada da Isra’ila, Indiya da UAE.

Zai kuma halarci wani taro na Kwamitin hadin gwiwa na kasashen Larabawa na yankin Gulf da suka hada da Masar, Iraki, da kuam Jordan a yayin ziyarar tasa a Saudiyya cikin watan Yuli mai zuwa.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*