?>

Bayanin Sheikh Ali Salman Akan Cika Shekaru Bakwai Da Daure Shi / Ba Zan Juya Ba Ya Ba

Babban magatakardar kungiyar Al-Wefaq ta kasar Bahrain ya fitar da wata sanarwa dangane da bikin cika shekaru bakwai da tsare shi a gidan yari na Al-Joo na kasar Bahrain.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - habarta cewa, kungiyar Al-Wefaq ta kasar Bahrain ta fitar da wani bayani da Sheikh Ali Salman ya fitar dangane da cika shekaru bakwai da tsare shi a gidan yari na Al-Joo.

Gundarin Bayaninsa:

Da sunan Allah
Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, bikin cika shekaru bakwai da kama ni ya zo, wanda kowa da kowa har da manyan jami’ai ya san irin zaluncin da aka yi mani, kuma Majalisar Dinkin Duniya a matsayin babbar hukuma a karkashin kudurin 2015/23 ta bayyana. a matsayin zalunci, kuma manyan kungiyoyin kare hakkin dan adam sun kira shi da zalunci.

Ina so in yi amfani da wannan damar in gode wa dukkan ’yan uwa da suka nuna goyon bayansu gare ni da neman kawo gyara da tabbatar da dimokuradiyya, ’yanci, mutunci da mutunta hakkin dan Adam, musamman iyalan shahidai, wadanda suka jikkata, ina mai subbatar hannayen kowannen su.

Tare da imani da dogaro ga Allah da taimakonsa a tafarkin nasara da kwanciyar hankali da neman zaman lafiya, zan kasance tare da ku masoya kuma ba zan juya ba daga kan wannan hanyar ba.

Wannan al'umma mai girma tana da hakkin samun mafi saukin hakki na mutane ma'abota daukaka da gudanar da harkokin jama'a ba tare da tsoma baki a cikin al'amuran jama'a ba, nesantar da Wasu tare nada daidaikun mutane, da su zamo Majibintan lamurra da mayar da mutane saniyar ware.

Sake fasalin siyasa da ake so shi ne moriyar tsare-tsare da al'umma kuma ginshiki da Kuma kwanciyar hankali don inganta yanayin tattalin arziki da rayuwa da ci gaba ta hanyar inganta ayyukan da ake yi wa 'yan kasa da kara samun kudin shiga da samun kwanciyar hankali ta fuskar siyasa.

Ka'idar soyayya, da kaunar juna da hakuri, (haduwar kai) tare rufe raunuka da fifita manyan muradun kasa shi ne abin da ke bude zukatanmu da hannayenmu ga abokanmu a kasar don tattaunawa da yarjejeniya kan ra'ayi na kasa da tsare-tsaren ayyukan da za su iya tasiri ga kasashen yankin da kuma samun duniya ta yi nasara kowa da kowa ya fahimtar bukatun kasa da 'ya'yanta.
Ina rokon Allah Ya ba ni nasarar bautar addini da kasa da al’ummar da ke cikinmu har karshen rayuwata.

Ofishin yada labarai na Sheikh Ali Salman
Janairu 12, 2022

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*