?>

Bangarorin Dake Rikici A Afganistan, Zasu Sake Ganawa Bayan Kasa Cimma Matsaya

Bangarorin Dake Rikici A Afganistan, Zasu Sake Ganawa Bayan Kasa Cimma Matsaya

Wakilan kungiyar Taliban da na gwamnatin Afghanistan sun ce za su hanzarta tattaunawar zaman lafiya yayin da kasar ke ci gaba da fadawa rashin tabbas.

ABNA24 : A wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar a ranar Lahadi, bangarorin sun ce za su sake haduwa da nufin hanzarta tattaunawar zaman lafiya bayan kwanaki biyu na tattaunawar da ba ta cimma gacci ba a birnin Doha, kamar yadda shafin gidan talabijin Al Jazeera ya rawaito.

Masu tattaunawar daga bangarorin da ke hamayya da juna, wadanda suka kasance a Doha tun ranar Asabar, sun ce "bangarorin biyu sun kuduri aniyar ci gaba da tattaunawa a wani babban mataki har sai an cimma matsaya".

Sanarwar ta kara da cewa "Za mu yi kokarin samar da kayayyakin jin kai a duk fadin Afghanistan."

Tsawon watanni kenan da bangarorin biyu ke haduwa a birnin Doha na kasar Qatar, ba tare da cimma wata nasara.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*