?>

Bangarori A Turkiyya Na Adawa Da Ziyarar Yariman Saudiyya

Bangarori A Turkiyya Na Adawa Da Ziyarar Yariman Saudiyya

A wani lokaci yau Laraba ne ake sa ran yarima mai jiran gado na Saudiyya, MBS, zai isa kasar Turkiyya a ci gaba da ran gadin da yake a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kafin Turkiyya Mohamed Ben Salman, ya ziyarci kasar Masar da Jordan.

Yayin ziyarar MBS, zai gana da shugaba Recep Tayyip Erdoğan, wanda kwanakin baya shi ma ya ziyarci kasar ta Saudiyya.

Wannan dai ya kawo karshen tsamin dangantakar data barke tsakanin kasashen biyu tun bayan kisan dan jaridan nan Jamal Khashoggi, a karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake Satambul a watan Oktoban 2018.

Kasashen biyu dai na fatan cin moriyar alakar kasuwanci a tsakaninsu bayan wannan sasancin.

Saidai bangarori da dama a Turkiyya sun soki ziyarar ta MBS, dake zuwa shekaru uku bayan kisan dan jaridan da ake zargin Ben Salman din da hannu a ciki.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*