?>

Australia Ta Ayyana Gabadayen Kungiyar Hezbollah A Matsayin Ta ‘Yan Ta’adda

Australia Ta Ayyana Gabadayen Kungiyar Hezbollah A Matsayin Ta ‘Yan Ta’adda

Gwamnatin Australia, ta sanya gabadayan kungiyar Hezbollah, ta kasar Lebanon a jerin kungiyoyin da take kallo a matsayin na ‘yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tunda farko dai matakin ya tsaya ne ga bangaren soji na kungiyar dake da karfin fada a ji a kasar ta Lebanon.

Babu wani dalili da kasar ta bayar na daukar wannan matakin, amma a cewar ministar cikin gida ta kasar, Karen Andrews, ta ce kungiyar gwagwarmayar dake samun goyan bayan Iran, na ci gaba da zama barazana da kuma goyan bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Amurka da Isra’ila dai sun jima da ayyana kungiyar Hezobollah a matsayin ta ‘yan ta’ada, amma wasu kasashe sun ki sanya bangaren siyasa na kungiyar a cikin jerin ‘yan ta’adda saboda fargabar kada hakan ya dabuga musu alaka da hukumomin kasar Lebanon.

Sanya kungiyar a jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda na nufin haramta Hezobollah a kasar da kuma hana duk wani mahaluki gudanar da harkoki da ita a kasar ta Australiya inda ‘yan Lebanon da dama ke da zama.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*