?>

Ana Gab Da Kammala Kada Kuri’a A Babban Zaben Iran

Ana Gab Da Kammala Kada Kuri’a A Babban Zaben Iran

A Iran, ana gab da kammala kada kuri’a a zaben shugaban kasar.

ABNA24 : Zaben na yau Juma’a ya kuma hada da na ‘yan majalisar jihohi da kananan hukumomi da kuma zaben cike gurbi na majalisar kwararru ta jagoranci.

‘Yan kasar kimanin miliyan 60 ne suka tantanci kada kuri’a a zaben.

Zaben wanda shi ne karo na 13 tun bayan juyin juya halin musulinci na kasar, ‘yan takara hudu ne ke fafatawa, bayan da uku daga cikin guda takwas da majalisar kare tsarin mulkin kasar ta sahale masu tsayawa takara a zaben suka janye a ranar Laraba.

Iraniyawa dai na zaben wanda zai maye gurbin shugaba Hassan Rohani, wanda ke kan kammala wa’adin mulkinsa na biyu kuma na karshe.

‘Yan takaran da ke fafatawa sun hada da Ebrahim Raeisi, da Mohsein Rezayi da Nasser Hemmati sai kuma Amir-Hossein Ghazi-zadeh-Hashemi.

Zaben dai ya gudana cikin kwanciyar hankali, da kuma matakai na yaki da annobar korona.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*