?>

An Yi Zanga zangar Kin Jinin Mulkin Sojoji A Chadi

An Yi Zanga zangar Kin Jinin Mulkin Sojoji A Chadi

A kasar Chadi, daruruwan mutane ne sukayi zanga zanga a safiyar Alhamis, domin nuna kin jinin sojojin dake rike da mulki a kasar, tun bayan mutuwar shugaban kasar Idriss Deby Itno.

ABNA24 : Wannan shi ne karon farko da masu mulki suka amincewa ‘yan adawa a kasar gudanar da zanga zanga.

Masu zanga zangar dai na nuna kin jinin sojin dake mulki dama tofin Allah-tsine ga kasar faransa.

Babbar jam’iyyar ta kasar ce wakit Tama, ta kira zanga zangar.

Duk da cewa dai zanga zangar bata samu halartar jama’a sosai ba, jagororin adawan sun sha alwashin sake fitowa a cikin makonni masu zuwa.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*