?>

An Yi Zanga Zangar Kin Jinin Faransa A Kasar Chadi

An Yi Zanga Zangar Kin Jinin Faransa A Kasar Chadi

A kasar Chadi, daruruwan mutane suka gudanar da zanga zangar kin jinin faransa, da kungiyar Wakit Tama ta kira.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Zanga zangar wacce ta samu goyan bayan daliban sakandare a yayinta an farmawa kaddarorin da wasu alamun faransa da dama, musamman gidajen shan main a Total mallakin faransa a birnin N’Djamena.

Masu zanga zangar na dauke da kwalayen dake dauke da rubutun ‘’ kin jinin faransa da ayyukanta a kasar.

Rahotanni sun ce jami’an kwaantar da tarzoma sun sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa masu zanga zangar.

Kungiyar ta Wakit Tama data kira zanga zangar ta ce ta yaba da yadda zanga zangar ta gudana.

Saidai wasu kungiyoyin fara hula sun janye daga zanga zangar wacce suka ce ta sabawa akidarsu ta kawo karshen rashin adalci da gwagwarmayar neman shinfida tsarin siyasa na gari a kasar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*