?>

An Sake Nada Amina Mohammed A Matsayin Mataimakiyar Babban Sakataren MDD

An Sake Nada Amina Mohammed A Matsayin Mataimakiyar Babban Sakataren MDD

A jiya talara ce aka sake nada Amina Muhammed na tarayyar Najeriya a matsayin mataimakiyar babban sakatren MDD a wa’adi na biyu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Leadership ta nigeriya ta bayyana cewa shugaban Muhammadu Buhari ya aikewa Amina Muhammad sakon taya murya da sake nadata a wa’adi na biyu, sannan ya godewa babban sakaren Majalisar Antornio Guterres da zaben da yayiwa Amina.

Mr Femi Adesina kakakin fadar shugaban kasa ne ya bayyana haka a jiya ya kuma kara da cewa shugaban kasar har'ila yau ya godewa babban sakataren da sake bawa Amina Muhammad wata dama ta yin khidima wa kasashen duniya a wannan babban mukamin na mataimakiyar babban sakataren Mjalisar.

Amina Muhammad dai ita ce ministan kare yanayi a gwamnatin Buhari kafin a zabeta kan kujerar da take rike da ita a halin yanzu a MDD.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*