?>

An Rufe Rejistar ‘Yan Takara A Zaben Shugaban Kasar Libiya

An Rufe Rejistar ‘Yan Takara A Zaben Shugaban Kasar Libiya

Hukumar zaben Libiya, ta kawo karshen karbar takardun ‘yan takara dake da sha’awar tsayawa zaben shugaban kasar na watan Disamba mai zuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kafofin yada labarai daga Libiyar sun ce ‘yan takara sama da 90 ne ciki har da mata biyu sukayi rejista domin tsayawa takara a zaben na ranar 24 ga wata mai zuwa, tun bayan da aka fara rejista a ranar 8 ga watan nan.

A wani lokaci a wannan Talata ce ake sa ran hukumar za ta bayyana adadin dindindin na ‘yan takaran da sukayi rejista, kafin ta bayyana wadana aka amince da takarar tasu bayan tantancewa.

Daga cikin ‘yan takaraen da suka ajiye takardunsu, da akwai Seif al-Islam Kadhafi, dan tsohon shugaban kasar Mu’ammar Ghaddafi, da Janar Khalifa Haftar mai karfin soji a gabashin kasar da wani yanki na kudanci, sai kuma tsohon ministan cikin gida na kasar Fathi Bachagha, da kuma shugaban gwamnatin rikon kwarya ta kasar Abdelhamid Dbeibah.

‘yan kasar sama da miliyan 2,83 ne aka kiyasta asu kada kuri’a a zaben na ranar 24 ga watan Disamba wanda ake ganin shi ne karon farko bisa tafarkin demokuradiyya a kasar.

Ana fatan Zaben dai zai samar da zaman lafiya a kasar da ta kasa samun gindin zama tun bayan guguwar neman sauyin da ta yi awan gaba da da mulkin tsohon shugaban kasar mirigayi Mu’ammar Ghaddafi a cikin shekarar 2011.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*