?>

An Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A Gambiya

An Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A Gambiya

A Gambiya, an bude yakin neman zaben shugaban kasar da za’a gudanar a ranar 4 ga watan Disamba mai zuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Zaben mai zuwa shi ne irinsa na farko tun bayan faduwar gwamnatin Yahya Jammeh wanda ya shugabanci kasar na tsawon shekaru 22, har lokacin da ya yi gudun hijira sakamakon matsin lamba daga kungiyar ECOWAS a watan Janairun 2017.

Daga cikin ‘yan takaren guda shida da zasu fafata a zaben, dake zaman zakaran gwajin dafi ga tsarin demokuradiyya na kasar har da shugaba Adama Barrow, wanda ya yi alkawarin mika mulki bayan riko na shekara uku.

Lamarin da ya kawo karshen dasawar dake tsakanin Adama Baroww da madugun ‘yan adawa na kasar a lokacin mulkin Yahya Jammeh, cewa da Ousainou Darboe, na jam’iyyar (UDP), wanda shi ma ke takara a zaben.

Har yanzu dai tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh, na da magoya baya a kasar, kuma ana ganin goyan bayan da ya baiwa dan takara Mammah Kandeh zai yi tasiri.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*