?>

Amurka Zata Aika Sojojin Dubu 17 Zuwa Kasashen NATO

Amurka Zata Aika Sojojin Dubu 17 Zuwa Kasashen NATO

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya aikewa majalisar dattawan kasar takardan bukatar aika sojoji 17,000 kari zuwa kasashen kungiyar tsaro ta NATO a kasashen Turai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tas na kasar Rasha ya nakalto wasu majiyoyin fadar white House na cewa shugaban ya bukaci “Majalisar dokokin kasar” wato Congress ta amince da bukatarsa ta aiko da karin sojojin 17,000 zuwa kasar Rasha don taimakwa kasar Ukraine a yakin da take fafatawa da kasar Rasha.

A halin yanzu dai yakin Ukrai ya shiga wata na hudu, amma kasar Rasha tana iko da kimani kasha 20 % na kasar Ukrain, mafi yawansu su a yankin Dambos na gabacin kasar.

Kasar Rasha dai ta bayyana cewa aiko da karin sojoji da kuma makamai zuwa kasar Ukraine wanda kasashen Amurka ta Turai suke yi, ba abinda zai kara sai tsawaita yakin.

A cikin watan Farbrainu na wannan shekarar ne kasar Rasha ta fada cikin kasar Ukrain a abinda da kira yaki na musamman don kubutar da yankunan Dambos na kasar Ukraine wadanda suke balle daga kasar, da kuma tabbatar da cewa ukrain bata shiga cikin kungiyar tsaro ta NATO ba.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*