?>

Amurka : Biden, Ya Amince Da Ikon Morocco Kan Yankin Saharaoui

Amurka : Biden, Ya Amince Da Ikon Morocco Kan Yankin Saharaoui

Shugaba Joe Biden, na Amurka ya amince da ikon Morocco, kan yankin Saharaoui, lamarin da ya kawo karshen mafarkin da masu fafatukar samar da yancin na Saharaoui ke yi na ko Biden zai dawo kan matakin da tsohon shugaba Donald Trump ya dauka.

ABNA24 : A ranar 10 ga watan Disamban bara ne Amurka karkashin gwamnatin tsohon shugaba Donald trump, ta amince da ikon Morocco kan yankin yammacin sahara.

Bisa wannan ne ita kuma kasar ta Morocco, ta amince dawo da alakar diflomatsiyarta da Isra’ila.

Amma da take sanar da hakan a makon jiya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Ned Price, ta ce Amurka na goyan bayan shirin MDD, na warware rikicin ta hanyar siyasa domin karshe tashin hankali.

Kuma kan hakan Amurkar na tuntubar dukkan bangarorin da batun ya shafa da kuma kasashen yankin domin kawo karshen rikicin.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*