?>

Al'ummar Tunusiya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Siyasar Shugaban Kasar

Al'ummar Tunusiya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Siyasar Shugaban Kasar

Dubban daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a kasar Tunusiya domin nuna kin amincewarsu da siyasar shugaban kasar Qais Sa’id ta bangare guda.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rahotonni sun bayyana cewa; Dubban daruruwan jama’a ne suka fito zanga-zangar gama gari a birnin Tunis fadar mulkin kasar karkashin jagorancin kungiyar National Salvation Front da ta hada kungiyoyi da jam’iyyun siyasa domin nuna adawa da siyasar bangare guda da shugaban kasar Qais Sa’id yake gudanarwa a kasar. Kungiyar ta fayyace cewa: Zanga-zangar tana matsayin yunkuri ne na kare tsarin dimokaradiyya da kin amincewa da abin da ta kira wasan kwaikwayo da shugaban kasar ya kira na neman gudanar da zaman tattaunawa da gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a.

Kungiyar ta jaddada yin kira kan kafa gwamnatin ceto kasar daga halin rudu da ta shiga da kuma fada da siyasar bangaren guda ta shugaban kasar wacce ta kira juyin mulki gami da jaddada goyon bayanta na neman ‘yancin kai ga bangaren shari’ar kasar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*