?>

Alhamdullah Kotu ta yanke hukunci Malam [H] zai fita Asibiti India don lafiyar sa

Alhamdullah Kotu ta yanke hukunci Malam [H] zai fita Asibiti India don lafiyar sa

Alhamdullah kamar yadda kotu ta ajiye yau litinin 5 ga watan Agusta 2019 zata zauna game da sauraren shari’ar su Malam[H] kuma zata yanke hukunci, gashi anyi zaman kuma kotu ta zartar da cewa Malam [H] zai iya fita asibiti a kasar India kamar yadda aka nema don neman lafiyar sa.

(ABNA24.com) Alhamdullah kamar yadda kotu ta ajiye yau litinin 5 ga watan Agusta 2019 zata zauna game da sauraren shari’ar su Malam[H] kuma zata yanke hukunci, gashi anyi zaman kuma kotu ta zartar da cewa Malam [H] zai iya fita asibiti a kasar India kamar yadda aka nema don neman lafiyar sa.

Wannan hukunci da kotu ta yanke, ta yanke shine bayan da lauyoyin gwamnati suka kasa kawo hujja akan ba sai an bar Malam [H] ya fita ba, yayin da lauyoyin dake kare Malam suka tabbatar da hujjoji na lizimcin kotu ta bar shi ya fita.

Tun bayan sanar da wannan hukuncin ne ‘yan uwa da dama suka fara gabatar da bukukuwa a birane daban daban don murnar wannan nasara.

Muna rokon Allah buwayi ya kara bamu wasu nasarorin ya kuma baiwa su Malam[H] lafiya su dawo cikin mu, kuma Allah ya tabbatarwa su Malam burin su ya karya makiyan su a ko ina./129


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*