?>

Afrika Ta Kudu : Karon Farko ANC, Ta Fadi A Zaben Magajin Birnin Johannesburg

Afrika Ta Kudu : Karon Farko ANC, Ta Fadi A Zaben Magajin Birnin Johannesburg

Jam’iyyar ANC, mai mulki a Afrika ta kudu, ta fadi a zaben magajin birnin Johannesburg, inda yanzu aka zabi wata daga bangaren ‘yan adawa da zata jagoranci da’irar babban birnin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : ANC, ta fadi ne a zaben kananan hukumomin kasar da aka gudanar a farkon watan Nuwamba, inda a tarihi ta samu kashi kasa da 50 cikin dari yayin zaben.

Tun a shekarar 1994, da kasar ta fara gudanar da zabe ta hanyar demokuradiyya, Jam’iyyar ANC ta Nelson Mandela, ce ke lashe zaben da gagarimin rinjaye, sai a wannan karon da ta fadi.

Wannan ya sanya, Mme Mpho Phalatse, ta jam’iyyar adawa ta (DA), ta kasance mace baka ta farko da zata jagoranci ma’aikatar magajin birnin Johannesburg, kuma mace ta farko tun daga shekarar 1946.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*