?>

Afirka Ta Kudu Ta Amince Da Amfani Da Sojoji 1,495 Don Taimakon MozambiqueWajen Faɗa Da ‘Yan Ta’adda

Afirka Ta Kudu Ta Amince Da Amfani Da Sojoji 1,495 Don Taimakon MozambiqueWajen Faɗa Da ‘Yan Ta’adda

Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ba da umurnin amfani da sojojin ƙasar su 1,495 don taimakon ƙasar Mozambique a faɗar da ta ke yi da ƙungiyoyin ta’addancin da suke da alaƙa da ƙungiyar nan ta Daesh (ISIS).

ABNA24 : Rahotanni daga ƙasar Afirka ta Kudun sun ce shugaba Ramaphosa ya ba da wannan umurnin ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa majalisar ƙasar wanda aka gabatar da ita ga ‘yan majalisar a jiya Laraba.

Umurnin shugaban dai na amfani da sojojin Afirka ta Kudun da ake kira da South African National Defence Force (SANDF) ya biyo bayan amincewar da ƙungiyar ƙasashen kudancin Afirkan SADC ta yi ne na tura sojoji zuwa Mozambique don faɗa da rikici da ayyukan ta’addancin da ke faruwa a ƙasar wanda ya faro tun shekara ta 2017 da yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.

Shugaban na Afirka ta Kudu ya ce sojojin na Afirka ta kudu za su taimaka wa gwamnatin Mozambique ɗin wajen faɗa da ayyukan ta’addanci da amfani da ƙarfi da ya addabi yankin Cabo Delgado na ƙasar.

Rikicin da ke faruwa a lardin Cabo Delgado da ke arewacin ƙasar Mozambique ɗin dai yayi sanadiyyar tarwatsewar dubun dubatan mutanen yankin sakamakon hare-haren ƙungiyoyin ta’addanci masu ikirarin jihadi.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*