?>

AfCFTA Za Ta Girmama Tsohon Shugaban Nijar Saboda Gudummawarsa Ga Ci Gaban Afirka

AfCFTA Za Ta Girmama Tsohon Shugaban Nijar Saboda Gudummawarsa Ga Ci Gaban Afirka

Кungiyar kula da yankunan kasuwancin bai ɗaya ta Afirka (AfCFTA) ta sanar da cewa a gobe juma’a za ta girmama tsohon shugaban ƙasar Nijar Mahamadou Issoufou saboda gudummawar da ya bayar wajen samar da ƙungiyar da kuma ci gaban kasuwanci a Afirka.

ABNA24 : Yayin da take sanar da hakan a wata ganawa da ta yi da manema labarai a birnin Accra na ƙasar Ghana, babban jami’ar hulɗa da jama’a ta ƙungiyar Mrs. Grace Khoza ta ce a yayin mulkinsa, shugaba Mahamadou Issoufou ya nuna ƙwarewar mulki da kuma burin ganin nahiyar Afirka ta ci gaba da a fagen kasuwanci.

Don haka tace bisa la’akari da hakan ne ƙungiyar ta ga ya dace ta girmama shi ta hanyar gina wani mutum-mutuminsa da kafa shi a babbar sakateriyar ƙungiyar da ke birnin na Accra na ƙasar Ghana.

Кungiyar ta ce ana sa ran shugabannin Afirka guda shida da kuma wasu tsoffin shugabannin Afirka su 2 ne za su halarci bikin na gobe.

Shugabannin da ake sa ran za su halarci bikin sun haɗa da na Togo, Faure Essozimna Gnassingbé Eyadéma, shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, na Burkina Faso, Roch Marc Christian Kaboré, na Demokraɗiyyar Kongo, Felix Tshisekedi da kuma shugaba ƙasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*