?>

Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Rikicin Afirka Ta Kudu Ya Kai Mutane 72

Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Rikicin Afirka Ta Kudu Ya Kai Mutane 72

Rahotanni daga ƙasar Afirka ta Kudu suna nuni da cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a ƙasar sakamakon tarzomar da magoya bayan tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma suke yi da nufin a sake shi daga gidan yari ya kai mutane 75, baya ga ɗaruruwan da ake tsare da su.

ABNA24 : A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ƙasar Afirka ta Kudun ta fitar ta ce adadin mutanen da suka rasa rayukansu tun daga lokacin da aka fara tarzomar ya kai mutane 72.

Sanarwar ta ce mafi yawan waɗanda suka mutun a lardunan Gauteng da Kwazulu-Natal sun rasa rayukan na su ne sakamakon turmutsutsin da ya faru a lokacin da mutane suke wawaso da sace kayayyaki a shagunan jama’a, a lokacin da dubun dubatan mutane suka yi dirar mikiya ga shaguna suna satar kayayyakin abinci, kayayyakin lantarki, tufafi da kayan shaye-shaye.

Wasu mutanen kuma sun mutu ne sakamakon harbin bingida da kuma fashewar abubuwa da suka faru yayin da mutanen suka kai hari kan bankuna da injunan cire kuɗaɗe ATM.

Rikicin dai ya ɓarke ne sakamakon ɗaure tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma da wata kotu ta yi inda magoya bayansa suka fito kan tituna don nuna rashin amincewarsu, lamarin da ya rikiɗe ya koma tarzoma da kuma sace kayayyakin gwamnati da na jama’a wanda wasu suka fassara cewa hakan ya faru ne sakamakon matsin da al’ummar ƙasar suke ciki.

A jiya Talata dai gwamnatin ta tura sojoji kamar yadda shugaban ƙasar Cyril Ramaphosa yayi alƙawari don taimaka wa ‘yan sanda kwantar da wannan tarzomar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*