?>

Aboul Gheit : Bai Kamata Duniya Ta Manta Da Bukatun Falasdinawa Ba

Aboul Gheit : Bai Kamata Duniya Ta Manta Da Bukatun Falasdinawa Ba

Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa, Ahmed Aboul Gheit, ya bayyana samar da mafita ga bukatun falasdinu a matsayin hanya daya tilo, domin wanzarda zaman lafiya da hadin guiwa a yankin gabas ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yayin wani taron kan makomar gabas tsa tsakiya, a taron kasa da kasa na Bakou a wannan makon, Aboul Gheit, ya bayyana cewa za’a iya cimma wannan ne idan Isra’ila ta mutunta dokokin kasa da kasa, ta dawo kan yarjejeniyar iyakokin da aka cimma a ranar 4 ga watan Juyin 1967, tare da amincewa da Kudus a matsayin babban birnin gwamnatin Falasdinu.

Mista Aboul Gheit, ya kuma ce ya damu akan yadda ba’a sanya bukatun al’ummar falasdinu ba a cikin jerin ababen dake damun danuwa.

Ya kara da cewa ba za’a samu makoma mai kyau ba, a yankin gabas ta tsakiya idan ba’a la’akari da bukatun al’ummar falasdinu.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*