?>

Abdollahian Da Guteress, Sun Zanta Kan Batutuwa Da Dama Da Suka Shafi Kasa Da Kasa

Abdollahian Da Guteress, Sun Zanta Kan Batutuwa Da Dama Da Suka Shafi Kasa Da Kasa

Babban sakataren MDD, Antonio Guteress, da ministan harkokin wajen kasar Iran, Hossein Amir Abdollahian, sun tattauna ta wayar tarho game da wasu batutuwa da suka shafi yankin da ma na kasa da kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yayin zantawar da ta wakana da yammacin jiya Juma’a, bangarorin sun tabo batutuwan da suka shafi halin da ake ciki a kasashen Yemen, Afghanistan da Ukraine, sai kuma batun tattaunawar neman dagewa Iran takunkumi.

Game da tattauanwar nukiliyar ta Iran, Abdollahian, ya ce Tehran na musayar sakwanni tsakaninta da Amurka, ta hanyar kungiyar tarayyar turai, amma ya dora alhakin tsaikon da aka samu kan halayen Amurka da kuma irin matakan kiyaya da take dauka kan Iran,wadanda su ne a cewarsa suka jefa tattaunawar cikin halin rashin tabbas.

Da ya tabo batun Yemen kuwa Mista Abdolahian, ya jadadda mahimancin karfafa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma, da kuma kawo karshen duk wasu matakai na killace Yemen.

Game da batun halinda ake ciki a Afgasnitan kuwa, ya ce akwai damuwa matuka game da al’amuran jin kai da tsaro a Afghanistan, wanda ana bukatar kafa gwamnati wacce ta kunshi ko wanne bangare na kabilu domin karshen karshen rikicin kasar.

Kan batun Ukraine kuwa, Iran ta bakin ministan harkokin wajenta, ta nanata adawa da duk wani salon a yaki, tana mai bukatar hada dukkan matakan siyasa da suka dace domin kawo karshen rikicin na Ukraine.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*