?>

A Yau Ne Ake Juyayin Shahadar Imam Ali (a) Wasiyyin Manzon All..(s) A duk Fadin Iran

A Yau Ne Ake Juyayin Shahadar Imam Ali (a) Wasiyyin Manzon All..(s) A duk Fadin Iran

A yau talata 21 ga watan Ramalan a nan kasar Iran wanda yayi dai-dai da 4 ga watan Mayu ake juyayin shahadar limami na farko daga cikin liamai masu tsarka daga iyalan gidan manzon All..(s).

ABNA24 : Kafin haka a daren shahadarsa tasa an gudanar da tarurruka a masallati da wurare masu tsarki a kasar inda malamai suka yi ta jawabai dangane da shahadarsa da kuma matsayinsa na magajin manzon All..(s) na gaskiya bayan wafatinsa.

A safiyar Jumma’a 19 ga watan Ramalan a shekara ta 40 bayan hijira ne wani bahawarije mai suna Abdurrahman bin Muljamil muradi ya sari Amirul mominina Aliyu dan Abitalib (s) a tsakiyar kansa da takobi wanda ya sa shi a cikin guba. Sannan bayan kwana biyu yay i shahada.

Kamar yadda ya zo cikin littafan tarihi khawarijawa ukku ne suka fita don kashe Imam Ali, da Mu’awi dan Abi Sufayan da kuma Amr bin Asi, amma ba wanda ya sami nasara kashe wanda aka wallaka masa sai ibn Muljamil Muradi.

Da haka kuma al-ummar musulmi ta yi rashin wand aba wanda yay i kusa da shi sai rashin manzon Al..(s).

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*