?>

A Kalla Mutane Biyu Ne Su Ka Halaka Sanadiyyar Wani Hari Da Aka Kai A Birnin Kabul Na Kasar Afghanistan

A Kalla Mutane Biyu Ne Su Ka Halaka Sanadiyyar Wani Hari Da Aka Kai A Birnin Kabul Na Kasar Afghanistan

Majiyar ‘yan sandan daga birnin na Kabul ta ambaci cewa; Da safiyar yau Asabar wani abu mai fashewa ya tarwatse a birnin Kabul na Afghanistan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da kuma jikkata wasu biyu.

ABNA24 : Majiyar ‘yan sandan ta kara da cewa; Bom din farko ya tashi ne da misalin karfe 8;00 akan titin Darulaman dake yammacin birnin na Kabul, yayinda bom na biyu ya tashi bayan mintuna 15 a yankin Karte-Parwan.

Mutane biyu ne su ka rasa rayukansu, yayin da wasu biyu su ka jikkata.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai harin.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni