10 Maris 2015 - 10:43
Kotu ta daure Matar Gbangbo na Cote D’Ivoir shekaru 20 a Gidan Kaso

Wata Kotu a kasar Cote d’Ivoire ta daure matar tsohon shugaban kasar Simone Gbagbo shekaru 20 a Gidan yari saboda samun ta da laifin zagon kasa ga harkokin tsaron kasar, da kuma mallakar kungiyar ‘yan ina-da-kisa da suka hallaka mutane kusan 3,000 tsakanin shekarar 2010 zuwa 2011

Shugaban kotun Tahirou Dembele ya bayyana hukuncin daurin ga matar da kuma daurin shekaru 5 ga dan tsohon shugaban Michel saboda rawar da ya taka a cikin tashin hankalin.

Yayin da take tsokaci kan hukuncin, Simone Gbagbo mai shekaru 65 ta ce ta yafewa wadanda suka zargeta domin kaucewa wani sabon tashin hankali a cikin kasar.

Baya ga Matar tasa haka ma an daure wani Dansa Michel dan haifen kasar Faransa da ya haifa da wata Mata shekaru 5 a Gidan Kaso akan samunsa da Hannu ga tashin hankalin da ya kashe mutane da dama.ABNA