Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Saudiyya ta sanya sabbin dokoki masu tsanani ga ma'aikata baƙi, waɗanda suka haɗa da cin tarar kuɗi har zuwa ɗauri.
Dangane da sanarwar ma'aikatar cikin gida da babban ofishin fasfo, Saudiyya tana sanya wa bakin haure da ke aiki da kansu, hukunce-hukunce har zuwa Riyal 50,000, ɗaurin watanni 6, da kuma fitar da su daga ƙasar. Jami'an Saudiyya suna ɗaukar wannan aiki a matsayin keta dokokin zama, aiki, da tsaron iyaka.
Dangane da wannan umarni, an kayyade hukunce-hukuncen bisa ga maimaita laifin a matakai:
- Karo na farko: Tara Riyal 10,000 na Saudiyya da fitarwa daga ƙasar.
- Karo na biyu: Tara Riyal 25,000 da ɗaurin wata ɗaya tare da fitarwa.
- Karo na uku da sauran lokuta: Tara Riyal 50,000 da ɗaurin watanni 6 tare da fitarwa daga ƙasar.
Jami'an Saudiyya sun jaddada cewa, waɗannan matakai ba su shafi ma'aikacin da ya yi laifi kawai ba; a'a, duk wani haɗin gwiwa da waɗannan mutane, ciki har da ɗaukar su aiki, sauƙaƙe aiki ba bisa ka'ida ba, kaiwa da komawarsu, ba da wurin kwana, ko rufe ayyukansu, suma za su fuskanci hukunci. A lokuta na haɗin gwiwa da masu laifi, tarar kuɗi na iya kaiwa har Riyal 100,000, da ɗaurin watanni 6.
………..
Ra'ayinka