5 Afirilu 2026 - 15:59
Source: ABNA24
Isra’ila Na Ci Gaba Da Murkushe Masu Zanga-Zanga Kin Jinin Yaki Da Iran A Tel Aviv

Masu zanga-zangar sun yi ta rera taken irin su "yaki ya isa haka", "babu tsaro da zaman lafiya da wannan gwamnati" da "Ministocin gwamnati (Majalisu) masu aikata laifukan yaki ne.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: 'Yan sandan Isra'ila sun murkushe masu zanga-zangar da kuma dukan a Tel Aviv, Kudus da Haifa wadanda masu zanga-zangar suna kira ne da a kawo karshen yakin da ake yi da Iran cikin gaggawa. Rahotonni sun ce, kimanin masu zanga-zangar dubu daya ne suka taru a dandalin Habima da ke tsakiyar birnin Tel Aviv, yayin da rundunar ta'addancin Isra'ila ta ba da damar mutane 150 kacal za su iya halartar zanga-zanga ko da ma za’a yi. Masu zanga-zangar sun yi ta rera taken irin su "yaki ya isa haka", "babu tsaro da zaman lafiya da wannan gwamnati" da "Ministocin gwamnati (Majalisu) masu aikata laifukan yaki ne.

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha