5 Afirilu 2026 - 15:36
Source: ABNA24
Yamen Ta Kame Jami’an Leken Asirin Mossad Da Aman Na Isra’ila

Yamen ta fitar da Sanarwar kama ‘yan leken asirin gwamnatin Isra’aila a Sanaa

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Tare da taimakon Allah da nasararsa, jami'an tsaro sun ba da rahoton kama wasu jami’ai da ke da alaka da aikewa da bayanai kai tsaye ga abokan gaba na Isra'ila ta hanyar jami’an leken asirin Aman da (Mossad) da sauran cibiyoyin Isra'ila.

Wadannan mutane sun gudanar da ayyukan leken asiri don goyon bayan abokan gaba na Isra'ila, ciki har da tattara muhimman bayanan soja da na tsaro, da tantance wuraren soji da na tsaro, da bayar da bayanai daban-daban da muhimman bayanai game da wuraren tattalin arziki da dama a kasar. Waɗannan mutane sun yi amfani da shirye-shiryen leƙen asiri da yawa da kuma tsarukan sadarwa na yanayin leƙen asiri don gudanar da ayyukansu. Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa nasarar da jami’an kasar Yamen suka samu da kuma taimakonsa wajen cimma wannan nasara, da kuma hadin kai, sa ido da wayar da kan 'ya'yan al'ummar Mujahideen Yemen, wadanda a ko da yaushe sun kasance wani shinge mai karfi a kan duk wani makirci da zagon kasa na makiya. Muna kira ga dukkan al’ummar Yamen da su sake tsananta sa ido don samun ƙarin kariya da yardar Allah, domin Al’umma suna taka muhimmiyar rawa wajen dakile makircin makiya na kai hari ga ƙasarmu ko ƙoƙarin hana ta goyon bayan al'ummar Palastinu da batutuwan al'ummar Musulunci da kuma tsayin daka da gwagwarmaya don hana zartuwar shirin sahyoniyawa na abin da suke kira "Babbar Isra’ila.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha