Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: "Binguir", ministan tsaron cikin gida na gwamnatin Sahayoniya mai tsattsauran ra'ayi ya kira da cewa: Al-Julani kamar kan maci ne kuma ya kamata a shirya kai masa hari da zai kashe. Yakin da ake yi da sabuwar Syria ya kusa.
Isra'ila tana ganin Jaulani yayi ƙasa a gwiwa wajen taimaka mata a yaƙin da ya ke yi Iran da Hizbullah don haka take kira da kawar da shi tana me ganin yana mata ungulu da kan zabo. A gefe guda kuma Jaulani ya aike da manyan kayan soji zuwa kan iyakar Iraki. Gwamnatin Abu Muhammad Jaulani, shugaban 'yan tawayen Syria, ya sanar a ranar Lahadin da ta gabata cewa, ya aike da sabbin kayan aiki da dakaru zuwa kan iyakar Syria da Iraki. "Ƙarin dakarun agaji sun isa kan iyakar Syria da Iraki a safiyar yau kuma an jibge su a kewayen yankin Al-Hari da ke kan iyakar," in ji wata majiyar soji a ma'aikatar tsaron Al-Jaulani. Ya ce kayan aikin sun hada da sojoji da dama da motocin soji da manyan makamai, kuma ya yi ikirarin cewa manufar matakin shi ne "hana duk wani kutsen tsaro a kan iyakar Syria da Iraki." Majiyar ta kuma ce kayan aikin da aka aika a yau su ne kaya karo na uku da aka tura zuwa yankunan kan iyaka tun bayan fara yakin Amurka da Isra'ila da Iran. Masana sun jaddada cewa Al-Jaulani ya aike da dakarun ne don aiwatar da umarnin Amurka da Isra'ila domin matsa wa dakarun Iraqi lamba, musamman dakarun Hashdush Sha'abi.
Majiyar da ke da alaka da Al-Jaulani ta bayyana cewa, "Dakarun gwamnati sun kama wasu Mutane na shahdush Shabi da Iran a cikin yankin Syria, wadanda dukkansu sun shiga cikin sirri ta kan iyakar Syria da Iraki." Bugu da kari, wata majiya da ke da alaka da Al-Jaulani ta ce "ya damu matuka" sakamakon hare-haren da jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami suka kai kan sansanonin Amurka a Syria. Majiyar ta yi ikirarin cewa, hare-haren baya-bayan nan da aka kai kan sansanonin Amurka da ke lardin Al-Hasakah da Deir Ez-Zor da ke Syria, sojojin Iraki ne suka kai su.
Ra'ayinka