Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Tashoshin Talabijin na Al-Manar da Al-Mayadin sun yi rashin manyan ma'aikatansu da suka shafe rayuwarsu suna watsa muryar gaskiya da 'yanci, da kare mutuncin Lebanon da tsayin dakar mutanen ta da gwagwarmaya wanda suka kasance ƙaya a kan hanyar masu aikata laifuka na duniya. Hotunan harin ta'addanci na gwamnatin Isra'ila na yadda Isra'ila ta kashe Ali Shoaib da Fatemeh Fatuni da Muhammad Fatuni mai daukar hoto na tashar Al-Mayadin jajirtattu kuma shahararrun 'yan jarida na Al-Mayadin da Al-Manar. Motar tawagar labarai ta Al-Mayadin da Isra'ila ta harba wani makami mai linzami.
Ofishin jakadancin na Iran ya yi ta'aziyya kan shahadar 'yan jarida uku na Lebanon: Mummunan laifukan sahyoniyawa, a wannan karon, ya kai hari ga kafofin watsa labarai na Lebanon ta hanyar kai hari ga Ali Shu'aib, dan jarida na Al-Manar, Fatimah Fatuni, ƴar jaridar Al-Mayadin, da kuma ɗan'uwanta Muhammad Fatuni, mai daukar hoto, wanda harin ya kai ga shahadarsu. Wannan mummunan hari ya faru ne a tsakiyar rashin cin nasarar ƴan ta'adda wajen cimma duk wata nasara a fagen daga da kuma kokarin da suke yi na boye gaskiya da kuma rufe muryoyin da ke rubuta laifukansu da bayyana karyar ikirarin nasu. Muna mika tsantsar ta'aziyya ga al'ummar yada labarai saboda wannan rashin.
Ra'ayinka