23 Maris 2026 - 13:01
Source: ABNA24
Dakarun Ƙungiyar Tsaron NATO Da Amurka Sun Tsere Daga Iraki 

Bayan hare-haren da dakarun gwagwarmayar Iraqi da na Iran ke kai wa sansanonin sojojin ta'addanci na NATO sun tsere daga kasar Iraqi 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sojojin Amurka da NATO sun tsere zuwa Jordan bayan da Ƙungiyoyin gwagwarmaya suka tsananta kai masu hari kan sansanoninsu da ke Iraqi ta hanyar mashigar kan iyakar Taribil, wanda Hukumar Yaki da Ta'addanci ta Iraki ta rakiya.

Dakarun Kungiyoyin gwagwarmaya ta Iraqi dai sun sha alwashin ci gaba da kai hare-hare saboda ɗaukar fansar jinin jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran har sai dakarun Amurka da NATO sun fice daga ƙasar da yankin baki daya. Wanda ke nuna tserewar da dakarun Amurka da NATO suka ba zai fishshe su ba domin a cen ma Urdin ba tsira su kai ba.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha